Ministan sufurin jiragen sama na kasa,Sanata Hadi Sirika Ya ce nan bada jimawa ba ,kanfanin jiragen sama na kasa zai fara gudanar da aiki.
Ministan ya baiyana cewa gwamnatin taraiyya ta kammala matakin farko na ganin kanfanin jirgin saman ya fara aiki, a yayin da yanzu ya rage samun lasisin zirga –zirgar da jiragen zai rika yi.
Da yake yiwa manema Labarai na fadar shugaban kasa jawabi, jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartawa na kasa a jiya, Ya ce tuni suka samu jiragen kuma har an yi masu fenti da tambarin kasar nan.