Kamfanonin jiragen sama na cikin gida a karkashin inuwar kungiyar masu kamfanin jiragen sama a Najeriya na neman gwamnatin tarayya ta ba su damar samun asisin shigo da man jiragen sama, mai suna JetA1.
Sun kuma bukaci gwamnati ta ba su damar samun chanjin kudaden waje daga babban bankin Najeriya domin baiwa masu sufurin damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na matafiya.
Shugaban kungiyar ta AON, Alhaji Abdulmunaf Yunusa ne ya yi wannan kiran a madadin mambobinsa yayin ziyarar ban girma da suka kai wa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, domin bayyana masa kalubalen da suke fuskanta.
Da yake mayar da martani, Keyamo ya yiwa masu kamfanonin jiragen sama alkawarin cewa ma'aikatar za ta hada kai da CBN domin ganin yadda za su rika samun chanjin kudaden waje cikin sauki.
Sai dai ya bukaci masu kamfanonin da su guji jinkirta tashin jirgin domin nan ba da dadewa ba zai fara aiwatar da dokar biyan diyya ga matafiya idan jirginsu ya yi jinkiri ba tare da wani dalili ba.