Gwarzon dan wasan real Madrid da kuma kasar Ingila Jude Bellingham ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi zura kwallaye a raga ta Kopa Trophy.
Yayin da mai tsaron raga na kasar Argentina Emiliano Martinez ya zama gwarzon mai tsaron raga na duniya.
Shi kuwa, Tauraron dan wasan kwallon kafar Argentina da kuma duniya baki daya, Lionel Messi ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’or, wanda hakan yasa ya sake lashe kyautar a karo na takwas, tun bayan da kasarsa ta samu nasarar daga kofin duniya a shekarar 2022.
Messi dan shekara 36 a duniya ya doke Karim Benzema wajen samun kyautar bayan da aka gwada kwazonsu na kakar wasannin data gabata, a lokacin da Messin ya kai Argentina ga daukar kofin kwallon kafa na duniya.
Kazalika itama Aitana Bonmati daga kasar Andalu ita ce gwarzuwar yar wasan kwallon kafar mata ta duniya, inda ta cinye kyautar ta Ballon d’or a bangare mata.
Bonmati ta doke abokiyar karawarta Alexia Putellas wajen samun kyautar.