Bayan ra'de-radin da aka yi dangane da takarar tsohon shugaba Jonathan, a karshe ta tabbata cewa zai yi takara karkashin jam'iyyar APC
Kasa da sa'o'i 48 bayan da ya barranta kansa daga yunkurin da wasu kungiyoyi suka yi na tunkuda keyar sa zuwa sake tsayawa takarar shugabncin kasa a shekarar 2023 mai zuwa, yanzu haka tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takarar a karkashin inuwar jam'iyya mai mulki ta APC.
A ranar Litinin ne, Jonathan yayi watsi da fam din tsayawa takarar da wata kungiya mai taken gamayyar Kungiyar Fulani makiyaya da al'umar almajirai suka ce sun saya masa.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan bai yiwa tsohon shugaban dadi ba, inda ya bayyana yunkurin nasu a matsayin wani abu da yayi kama da cin fuska, domin kuwa a cewar sa, bai kamata kungiyar ta siya masa fam din ba tare da izinin sa ba. Sai dai yanzu haka, Jonathan yayi mi'ara koma baya akan waccan turjiya da yayi tun da fari.
Wata majiya dake da kusanci da Jonathan, wacce ta bukaci a sakaya sunan ta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa, tabbas, tsohon shugaban kasar ya koma jam'iyya mai mulki kuma tuni yayi rajista a mazabar sa dake garin Utuoke a jihar Bayelsa.
Majiyar ta kuma kara da cewa ana sa ran Jonathan zai gabatar da cikakken fam din da kungiyar makiyayan ta siya masa ga shalkwatar jam'iyyar APC a ranar alhamis.
Majiyar har ila yau, tace tuni tsohon shugaban kasar ya samu goyon bayan da yake bukata daga wajen masu zaben 'yan takara na jam'iyyar ta APC a jihohi 36 cikin tarayyar kasar nan.
Kazalika, ta shaidawa wakilin siyasa na kamfanin dillancin labarai na kasa a daren laraba cewa, wasu shugabannin kasashen Africa sun kira Jonathan a ranar Litinin, inda suka bashi shawarar sake neman zama shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa.
Yace "akalla manyan shugabannin nahiyar Africa guda 3 ne suka kira shi akan batun, kuma dukkan su sun bukaci ya shiga yakin neman zaben a shekara mai zuwa".
Ya kara da cewa, guda daga cikin su, ce masa yayi, "bai dace ba ace ya karade kasashen Africa domin tabbatar da zaman lafiya, sannnan yayi watsi nauyin shugabanci a kasar sa".