Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya yabawa shugaba Bola Tinubu kan karfin shugabancinsa, musamman a rikicin da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar ya haddasa.
Tinubu a matsayinsa na shugaban ECOWAS ya yi gaggawar yin Allah wadai da juyin mulkin tare da sanya wa sabuwar gwamnati takunkumi.
Da yake mayar da martani a wata sanarwa da fadar White House ta fitar a rana ta biyu a taron kasashen G20 a India, Biden ya yabawa Tinubu kan yadda yake kiyaye doka a Nijar da kuma manufofinsa na tattalin arzikin kasa a Najeriya.
Ya godewa Tinubu kan kare dimokuradiyya da kiyaye doka, yana mai jaddada kudurin Amurka na karfafa dadaddiyar dangantakarta da Najeriya.