An hango wani jirgin saman Nigeria Air a filin jirgin saman Addis Ababa Bole dake kasar Habasha.
Rahotanni sunce jirgin zai sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja da yammacin yau Juma’a.
Idan dai za a iya tunawa, ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa jirgin saman Nigeria Air yana kan hanyarsa ta zuwa Najeriya cikin kasa da sa'o'i 24.
Sai dai kuma wannan ci gaban ya haifar da ce-ce-ku-ce, yayin da masana da masu ruwa da tsaki suka nuna shakku kan dalilin da ya sa za'a kaddamar jirgin sa'o'i 72 gabanin karewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.