Daya daga cikin kanfanonin jiragen saman da suka yi jigilar Alhazan Najeriya a Aikin Hajjin Bana, Max Air , Yace zai fara jigilar dawo da alhazan kasar nan daga kasa mai tsarki a ranar Asabar
Wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Dahiru ya fitar jiya a Abuja, Yace Alhazan jihar Borno sune za’a fara kwasowa zuwa gida Najeriya.
Hukumar aikin hajji ta kasa, ta dora alhakin jigilar Alhazai dubu 16 da suka fito daga jihohi 13 akan kanfanin jiragen sama na Max Air a aikin hajjin bana.
Jihohin sun hada da Borno sai Adamawa da Bauchi da Gombe da Taraba da Niger da Kogi Da jihar Kwara Da Jigawa da Katsina da Benue sai Jihar Filato da Kuma jihar Nasarawa.