Kanfanin jiragen sama na Emirates zai rage zirga-zirgarsa a kasar nan sakamakon gazawarsa wajen bawa gwamnatin Najeriya Harajin Dala Milyan 85.
Kanfanin ya baiyana haka ne, ta cikin wata wasika da ya aikewa ministan sufurin jiragen sama na kasa, Hadi Sirika, a ranar 22 ga watan da muke bankwana dashi.
Mataimakin shugaban shiyya na kanfanin jiragen saman Emirates, Sheik Majid Al Mualla, Yace rage zirga-zirgar kanfanin a kasar nan zata fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Gobe.
Sanarwar ta kara da cewa za’a rage sauka da tashin jiragen saman Emirate daga kaso 11 bisa 100 zuwa Kaso 7 bisa 100 a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed dake Ikko.