Shekaru uku bayan da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya fado kan wani gini da ke unguwar Opebi a jihar Legas inda ya yi sanadin ajalin mutane 3 a cikinsa, a jiya talata wani jirgi mai saukar ungulu ya sake fadowa a birnin na Ikko.
An yi sa'a, hadarin na jiya wanda ya faru a unguwar Oba Akran a Ikeja dake jihar Legas bai yi ajalin kowa ba kamar na watan Agustan 2020.
Jami’an Hukumar Ba da Agajin gaggawa ta Jihar Legas LASEMA sun ce jirgin ya kama da wuta lokacin da al’amarin ya faru.
LASEMA ta kuma ce an ceto mutane hudu da suka hada da matukin jirgin da ransu, inda aka kai su wani asibiti da ke kusa.