Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, Ya ce hukumomi dake kula da harkokin sufurin jiragen sama a kasar nan zasu fara tilastawa kanfanonin jiragen sama biyan diyya ga fasinjojin da suka fuskanci tsaikon tashin jirginsu, ko kuma aka soke tashin jirgin baki dayansa, daga watan janairun sabuwar shekara ta 2024.
Ministan ya baiyana haka ne a lokacin da ya baiyana gaban hadakar kwamitin kula da sufurin jiragen sama na zaurikan majalisun dokokin kasa, domin kare kudirin kasafin kudin ma’aikatarsa.
Ya ce za’a yi ragin kudin tikiti ga fasinjojin da suka fuskanci tsaikon tashin jirginsu a wani bangare na biyansu diyya.
Ministan ya kuma bada tabbacin cewar za’a rika wallafa sunayen jiragen da suka yi jirgin tashin fasinjojinsu a kafafen yada labarai a kowane mako.