On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jihar Kano Na Bukatar Naira Biliiyan 6 Domin Samar Da Kujeru A Makarantun Firamare Da Sakandire - Doguwa

Kwamishinan ilimi, Alhaji Umar Doguwa, ya ce jihar Kao na bukatar Naira biliyan 6 don samar da kujerun zama ga daliban makarantun firamare da sakandare.

Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an asusun tallafawa kananan yara na majalissar dinkin duniya UNICEF, ofishin dake kula da Kano, karkashin jagorancin Rahama Rihood Mohammad Farah, a ofishinsa.

A cewar Doguwa, mafi akasarin yara miliyan 5.2 da ke makarantun Kano ba su da kujeru da tebura, inda ya ce a wata makaranta da ke Dawakin Tofa da ke da dalibai dubu 5 da 618, dukkan su na zaune a kasa.

Ya ce baya ga karancin kujeru, akwai kuma matsalolin karancin malamai da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, don haka ya yi kira ga kungiyoyin raya kasa da su tallafa wajen maganin matsalolin

Tun da farko, shugabar ofishin UNICEF a Najeriya, Rahama Farah, ta jaddada kudirin UNICEF na yin aiki tare da gwamnatin jihar Kano don magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.