A yayin da har yanzu, mafi akasarin Daliban Jami’oi basu kaiga murmurewa daga lahanin da yajin aikin kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, da aka janye kwanan nan yayi masu ba, Sai dai kuma a iya cewa, ta wani bangaren yajin aikin ya zama wani abun tagomashi ga wadansu daliban a nan Kano.
Daliban, Sun baiyana wasu daga cikin kalubalen da suka fuskanta daga bangaren abokansu da kuma sauran jam’ar gari, dama yadda suka yi amfani da lokacin yajin aikin , wajen kirkirar wata manhaja da zasu magance kalubalen.
Irin wadannan kirkire-kirkire da Daliban suka bijiro dasu a lokacin da ake yajin aikin na ASUU, sune abubuwan da rahotonmu na musamman a wannan makon, da wakilinmu, Kamaludden Muhammad ya hada mana yayi duba a kai.
Ga shi kuma da cigaban rahoton da ya hada mana.
Latsa kasa domin jin cikakken rahoton