Tun daga farkon watan Augustan bana zuwa yanzu, kimanin mutane 134 ne suka rasa rayukan su sannan aka samu rabewar hanyoyi, inda kuma gonaki da makarantu suka shafe a sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a yankuna da dama dake jihar Jigawa.
Jihar dake da fadin kasa kilomita dubu 23 da 154, kaso 80 na alummar jihar sun dogara ne da yin noma da kuma kiwon dabbobi, gonaki da dama ne ambaliyar ruwan tayi awon gaba dasu , al’amarin dake barazana ga tattalin arzikin jihar.
Wadannan matsaloli sune suka jaa hankalin wakilan mu Nura Haruna Mudi da Caleb Jacob wajen kai ziyarar gani da ido zuwa jihar dake arewa maso yammacin kasar nan domin samun sahihan bayanai a cikin rahoton mu na musamman na wannan makon.
Ga kuma Kamaluddeen Muhd dauke da fassarar rahoton nasu.
Latsa sautin dake Kasa domin jin Cikakken Rahoton...