On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Janar Mahamat Idriss Deby Itno Ya Nada 'Yan Majalissar Dokoki Sama Da 100

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a kasar chadi Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya nada karin mutane 104 a matsayin wakilai a cikin zauren majalisar dokokin kasar, kamar dai yadda ya dauki alkawari bayan kammala taron tattauna matsalolin kasar da aka yi a birnin Doha na kasar Qatar.

Taron daidaita alkiblar kasar  wanda ya gudana a watan da ya gabata ya bada shawarar kara yawan mambobin majalisar wucin gadin, da ke aiki a matsayin majalisar dokoki, daga 93 zuwa 197.

A cikin kudurin dokar da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya gani, Janar Deby ya nada “karin mambobin majalisar  104, wadanda suka hada da tsoffin ‘yan jam’iyyar adawa, da ‘yan tawayen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Agusta da kuma wakilan kungiyoyin farararen hula.

Sai dai duk da haka, akwai wasu 'yan adawa da kungiyoyin 'yan tawaye da suka kauracewa taron saita alkiblar kasar, inda suke nuna rashin amincewarsu.

Janar din dan shekara  38 ya karbi ragamar mulki a watan Afrilun 2021 bayan an kashe mahaifinsa, wanda ya yi mulkin Chadi tsawon shekaru 30 a lokacin da ya jagoranci rundunar sojin kasar don kai farmaki kan 'yan tawaye .