Jam’iyyar PRP ta gaza tasarrafi da kudadenta sakamakon sabon tsarin harkokin kudi a Najeriya, ta kuma yi barazanar daukar matakin shari'a kan CBN a gaban Kotu.
PRP dai ta zama ta farko da ta fara ji a jikinta ta hanyar tasirin sabon tsarin kuɗi na babban bankin kasa CBN a tsakanin jam’iyyun siyasa, ta kuma yi tsokaci kan yadda tsarin ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalu, inda ta ce ta gaza samun kudaden da ta adana domin zabe mai zuwa.
Saboda haka jam’iyyar ta yi barazanar neman diyya a gaban kotu daga CBN.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Alhaji Falalu Bello, ya bayyana haka a lokacin gabatar da kundin manufofin jam'iyyar ga manema labarai a Abuja.
Jaddawalin manufofin dauke da kudurori shida, ya tabo batun sake fasalin tattalin arziki da inganta ilimi da bunkasa hadin kan kasa da tsarin tarayya na gaskiya da inganta tsaron kasa da farfado da masana'antun hakar mai da man fetur da iskar gas da ma'adanai.
Bello ya ce janye sama da Naira Tiriliyan 2 da suke jagawwa a hannun jama'a da kuma buga Naira biliyan 300, shine makasudin hamudani da ake fuskanta a Najeriya.