Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Samuel Ayanwu, Yace gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, Ya sadaukar da kansa matuka wajen samun dorewar cigaban jam’iyyar.
Ta cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Owerri na jihar Imo a yau, kakakinsa, Ikenna Onuoha, Yace bai taba yin wasu kalamai na sukar gwamna wike ba, dangane da rikicin ciki gida da jam’iyyar PDP ke ciki.
Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Ya kara da cewa rahotannin da wasu kafafen yada Labarai suka wallafa, wanda kecewa ya nisanta kansa da gwamna wike basu da kanshin gaskiya a cikinsu, sai dai kawai an kirkire su ne domin haddasa rabuwar kawuna a tsakaninsu.
Sanarwar ta kara da cewa, Mister Anyanwu ya umarci lauyoyinsa su fara shirin daukar matakin shari’a akan wanda ya wallafa Labarin.