Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulkin kasa da boye sabbin takardun kudi da aka sauyawa fasali, domin siyan kuri’a a zabe mai zuwa.
A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na kasa,Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahadi,Ya ce kunchin da jam’iyyar APC ta jefa kasar nan, zai zama tarihi, idan aka zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa.
Jam’iyyar ta PDP ta yi kira ga babban bankin kasa, da yayi hankali da yadda jama’ar kasar nan suka samu kansu a ciki.
Bugu da kari ta yi kira ga Bankunan kasar nan dasu dauki matakan da suka dace na kawo karshen matsalar rashin kudi da jama’a suke a ciki, da kuma sanya ido kan yadda ake rarraba kudin a tsakanin jama’ar kasa.