Jam'iyyar PDP ta caccaki jam'iyyar APC akan zaben tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.
A hukumance jam’iyyar APC ta tabbatar da nadin Ganduje da mai magana da yawun majalisar dattawa ta tara, Sanata Ajibola Basiru a jiya don maye gurbin tsohon shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakatare jam’iyyar, Iyiola Omisore.
Sai dai Jam’iyyar PDP, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, a Abuja ranar Alhamis, ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda bai chancanta ba.
Sanarwar ta ce zaben Ganduje duk da zargin cin hanci da rashawa da ake zarginsa da aikatawa ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC wata mafaka ce ta cin hanci da rashawa da boye masu karbar rashawa da kuma masu wawure dukiyar kasa.
Yayin da jam'iyyar PDP ke sukar nadin Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC, shi kuwa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yaba da matakin.
Sanata Barau, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ismail Mudashir ya fitar, ya ce bisa nadin tsohon gwamnan a shugabancin jam’iyyar APC, za a mayar da jam’iyya mai mulki wani matsayi tare da karfafawa dukkan mambobinta.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kara da cewa, bisa dimbin gogewar tsohon gwamnan jihar Kano, za’a samu ingantuwar tsarin magance rikice-rikice na jam’iyyar APC domin rage rigingimun cikin gida.