Wata Babbar Kotun taraiyya mai zamanta a birnin Abeokutan jihar Ogun, ta soke daukacin zaben fidda gwani na ‘yan takara daban-daban da jam’iyyar PDP ta gudanar, Gabanin Babban zaben shekara mai zuwa.
Mai shari’a O.O Oguntoyinbo ne ya bada umarnin, lokacin da yake zartar da hukunci akan shari’ar, wadda wasu ‘ya’yan jam’iyyar Taiwo Olabode idris da Kehinde Akala da kuma Alhaji Ayinde Monsuri suka shigar gaban kotun, sun kalubalantar sunayen wakilan jam’iyyar da aka yi amfani dasu a yayin zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gabatar.
Zaben fidda gwanin da kotun ta soke sun hada, Dana Gwamna sai yan majalisar dattawa da ‘yan majalisar wakilai da kuma na yan majalisar dokokin jihar ta Ogun, A bisa haka ne kotun ta bada umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda yan takara nan da kwanaki 14 masu zuwa.
Bugu da kari kotun ta haramtawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta cigaba da aiyana Hon Ladi Adebutu a matsayin dan takarar gwamnan jihar ta Ogun karkashin jam’iyyar PDP.