Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP, Ya kafa wani kwamiti da zai sulhunta Dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike.
Tsohon dan majalisar dokokin taraiyya sannan kuma wakili a cikin kwamitin dattawan jam’iyyar Sanata Abdul Ningi ne ya baiyana haka lokacin da yake yiwa manema Labarai jawabi, bayan kammala zaman kwamitin a Abuja.
Sanata Ningi wanda bai baiyana wa’adin da aka bawa kwamitin ba, Yace ana saran kwamitin zai dinke barakar dake tsakanin bangarorin biyu domin samun zaman lafiya.
Dangane da bukatar shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga kan kujerarsa, Sanata Ningi yace kwamitin bai tattauna wannan maganar ba.