Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaban jam’iyyar Apc na kasa, Abdullahi Adamu, kan Kalaman da yayi na cewa gwamnatin tarayya zata iya cigaba da ciwo bashi daga yanzu har Illa Masha Allah.
A yayin wata hira da aka yi dashi ta cikin wani shiri a gidan talabijin na Trust a ranar Litinin, Adamu ya ce kasashe irin su Amurka da Ingila suna karbar lamuni daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin biyan bukatunsu.
Ya kara da cewa kamar sauran kasashe, Najeriya na iya cin bashi a kowane lokaci domin bunkasa samar da ababen more rayuwa.
Da yake mayar da martani kan kalaman da shugaban jam’iyyar APCn yayi, kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce bai dace shugaban jam’iyyar ya kafa hujja da cewar ana ciwo bashin ne domin yin abubuwan da zasu amfani kasa.
A yanzu haka dai bashin kasashen waje da ake bin Najeriya ya haura tiriliyan 41 da bilyan 60.