Jam’iyyar PDP ta lashi takobin rubutawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta kokenta a yau Talata, domin neman a sake gudanar da sabon zabe, wanda zai bada damar canza ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas guda 27, da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jiya.
A ranar Litinin ne yan majalisa 27 na jam’iyyar PDP suka sanar da komawarsu jam’iyyar APC, tare da yin barazanar yin fatali da bukatun da gwamnan jihar Ribas Sim Fubara ya gabatar masu.
Ana zargin sauyin shekar da ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi, nada alaka da yakin cacar baka dake wakana tsakanin gwamnan da ministan Abuja Nyesom Wike.
Da yake tsokaci kan canza jam’iyyar da suka yi, Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Olugunagba, ya fadawa manema labarai a daren jiya cewar, Jam’iyyar zata yi amfani da matakan da suka dace domin kwato kujerun nata.
Ya kuma aiyana kujerun ‘yan majalsiar guda 27 da suka canza jam’iyya a matsayin wadanda babu kowa a kansu, kamar yadda yake bisa sashi na 109 daya cikin baka da Ga cikin baka, na kundin tsarin mulkin kasa da aka yiwa gyaran fuska.