![](https://mmo.aiircdn.com/370/627bfa73debec.jpg)
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano, Ta yi barazanar janye goyon bayan ta akan yarjejeniyar samar da zaman lafiya data saka hannu akan ta, saboda zargin da ta yi na cewar jami’an ‘yansanda da kuma gwamnatin jihar kano na kulla wata makarkashiya na tsoratar da ‘yan takarar dake cikin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta yi zargin cewar rundunar ‘yansandan jihar Kano ta karbi wani umarni daga hannun gwamnatin jihar Kano, inda suka yi wani shiri ta karkashin kasa domin a rika kama jiga-jigan jam’iyyar ta NNPP a kananan hukumomin jihar Kano 44.
Dan takarar sanatan kano ta Arewa a karkashin jam’iyyar ta NNPP, Dr Baffa Bichi ne ya baiyana haka a yayin wani taron manema Labarai da aka shirya a sakatariyar jam’iyyar dake nan Kano.
Ya kuma yi ikirarin cewar suna da hujjoji na sunayen ‘yan jam’iyyar NNPP da za’a kama.
Har kawo wannan lokaci dai rundunar ‘yansandan jihar kano bata mayar da martani akan zargin ba.