Manyan jam’iyyun hamaiyya na kasar sun fara mayar da martani kan kiran da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi, inda ya baiyana cewar kamata ya yi jam’iyyun Hamaiyyar su hade wuri daya domin karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC.
Idan ba’a manta ba, Atiku Abubakar ya baiyana bukatar yin sabuwar Majar ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin majalisar bada shawarwari a tsakanin jam’iyyu ta kasa a Abuja ranar Talata.
A martanin da jam’iyyar Labour ta yi ta hannun mukaddashin sakataren yada labaranta Obiora Ifoh, Ya baiyana yunkurin hadewar wuri daya a matsayin wani abu da ya d ace, wanda kuma ya kamata ayi nazari kansa.
Haka zalika itama jam’iyyar NNPP ta hannun sakataren yada labaranta na kasa Yakubu Shendam, ya baiyana kiran da Atikun ya yi a matsayin abun jan hankali sannan kuma magani ne bayan mutuwa.
Ya kara da cewar za’a yadda da bukatar Atikun ne kadai idan har zai goyi bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya karbo mulki daga hannun jam’iyyar APC a shekarar 2027.