Jam’iyyar LP reshen jihar Ogun, Ta kori Babban daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Dr Doyin Okupe daga cikinta.
An kori Okupe tare da wadansu mutane 10 daga cikin jam’iyyar, bayan an zarge shi da kin sabunta shaidarsa ta zama dan jam’iyyar a watanni shida da suka gabata, wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
An cimma wannan matsaya ne a yayin taron da jam’iyyar ta gudanar a sakatariyarta dake birnin Abeokuta a ranar Alhamis, inda suka yi kira da a gaggauta samar da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar na yankin Arewa, domin tabbatar da samar da daidaito da kuma ingantaccen tsari na siyasa.
Shugaban jam’iyyar Labour, reshen jihar, Michael Ashade, Ya ce an dauki matakin ne domin ladabtarwa, sannan kuma ya zargi Mister Doyin Okupe da raba kan jam’iyyar a jihar.