Sakamakon sauyin da aka samu, Jam’iyyar APC mai mulkin kasa, ta sanar da cewa zata fara gangamin yakin neman zabenta na shugaban kasa daga ranar 28 ga watan Satumbar bana.
A yaune ake saran kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa a karkashin shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu, zai yi wata ganawa ta musamman domin domin tsayar da matsaya guda da kuma sanar da lokacin da za’a yi taron kwamitin kolin jam’iyyar na kasa.
A taron kwamitin na baya da aka yi cikin watan Afrilu ta bawa kwamitin wa’adin kwanaki 90 domin ya fitar da matsayarsa . Wata majiya daga kwamitin ta baiyana cewa ganawar gaggawar ta zama wajibi domin baiyana abunda aka tsaya a kai, a karkashin sanata Abdullahi Adamu.