On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Zata Dawo Jihar Kano - Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa Sanata Barau

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ke fatan jam'iyyar APC za ta kwato jihar Kano daga hannun jam'iyyar NNPP.

Jam'iyyar APC a Kano dai  tana kotun sauraron kararrakin zabe tana kalubalantar nasarar Gwamna Abba Kabiru Yusuf.

Da yake magana a lokacin da tawagar mataimakan shugabannin kananan hukumomi a Kano suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba, Jibrin ya ce yana da kwarin gwiwar cewa kotun za ta yanke hukunci domin tabbatar da jam’iyyar APC.

Ya kuma bukaci wakilan da su hada kai su yi aiki tare, ya kara da cewa lokaci ya yi, jam’iyyar za ta dawo jihar Kano.