Jam’iyyar APC ta kalubalanci Sanatocin da suka fito daga yankin arewacin kasar nan, dake neman kujerar shugabancin majalisar dattawa, Inda ta yi kira a gare su dasu jingine wannan aniya tasu, domin tabbatar da adalci.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa,Salihu Lukman da kuma Kakakin jam’iyyar Bala Ibrahim,Sunce duk wani sanata da ya fito daga yankin arewacin kasar nan,kuma yake neman kujerar shugaban majalisar dattawa,To babu shakka bai mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.
Idan za’a iya tunawa,Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar da suka fito daga yankin Kudu maso kudu da kuma Kudu maso gabashin kasar nan,Sun bukaci a basu kujerar shugabancin majalisar domin tabbatar da adalci ga kowane bangare na kasar nan.
Kazalika sunyi ikirarin cewar matakin shine zai nuna cewar ana yi da kowane bangare na kasar nan, La’akari da yadda jam’iyyar ta APC ta bayar da tikitin takarar shugaban kasa dana mataimakinsa ga Musulmi.