Kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa , Ya rarraba mukaman shugabancin zauren majalisar dokoki ta kasa na Goma da za’a kaddamar, a tsakanin shiyyoyin kasar nan.
A cewar wata sanarwa da Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka ya fitar a ranar Litinin, Ya ce yadda aka raba mukaman ya kunshi, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio daga jihar Akwa Ibom, wanda ya fito daga shiyyar kudu maso kudancin kasar nan,Sai mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin daga nan jihar Kano, wanda ya fito daga shiyyar Arewa maso yamma a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Sauran sune, Kakakin majalisar wakilai,Hon Abbas Tajjudden daga jihar Kaduna wanda shima ya fito daga shiyyar Arewa maso yamma, Sai kuma mataimakisa Hon. Ben Kalu daga Jihar Abiya, wanda ya fito daga shiyyar kudu maso gabashin kasar nan.
Sanarwar ta biyo bayan tattaunawar da kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC na kasa ya yi, da kuma ganawar da suka yi da zababben shugaban kasa Bola Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki, kan yadda za’a rarraba mukaman.