Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Ta gargadi gwamnatin jihar Kano kan duk wani yunkuri na rushe sabbin masarautun Kano da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samar, Inda ta ce matakin zai gurgunta zaman lafiyar da ake da shi a jihar Kano.
A ranar Talatar data gabata ce, Wata Kungiya mai suna ‘Yan Dan gwanlen jihar Kano, ta aike da wasika ga zauren majalisar dokokin jihar Kano, inda take neman a yiwa dokar data kafa sabbin masarautun jihar Kano gyaran fuska, Masarautun sun hada da Gaya sai Rano da Karaye da Bichi, Sannan kuma sun nemi a dawo da tsohon sarkin kano Mohammadu Sanusi na biyu.
To sai dai a sanarwar da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Ahmad Aruwa ya fitar, Ya baiyana mamakinsa kan yadda kungiyar bata yi korafi ba a lokacin da aka kirkiri sabbin masarautun, Inda ya ce kamata ya yi a rika girmama masarautu.
Jam’iyyar ta APC ta sharwaci gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusufu na jam’iyyar NNPP da ya yi taka tsan-tsan sannan kada ya bari a yi amfani da shi wajen yin abunda zai tada zauni tsaye a jihar Kano.