On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Ta Ce Zafin Shan Kaye Ne Ke Damun Atiku Abubakar

Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata karkashin jam’iyyar PDP, da ya rungumin ‘kaddarar shank aye a zaben shugaban kasa da ya gabata.

 

 A  yayin wani taron manema labarai da  Atikun ya shirya a jiya, Ya yi kira ga sauran ‘yan takarar shugaban kasa  zaben da  ya gabata  dasu mara masa baya, domin yaki da amfani da takardun kammala  karatu  na bogi, da yake zargin shugaban kasa  Bola Tinubu na  amfani dasu.

To sai dai a martanin da jam’iyyar  APC  ta mayar dangane da shirya  taron manema labaran, ta hannun kakakinta, Felix Morka, Ta baiyana  cewar taron manema labaran a matsayin  na fanko  wanda kuma  bashi  da wasu  kwararan hujjoji daya dogara dasu.

Ya  kuma ce  tuni aka wanke shugaban kasa  Tinubu daga zarge-zargen da ake masa, kasancewar makarantar ta tabbatar da cewar  shugaban kasar ya yi karatu a cikinta.

Kakakin jam’iyyar  APCn na kasa  ya baiyana yunkurin  da Atikun ke yi a matsayin  zafin shan kaye saboda rashin samun zama shugaban kasa.