Jam’iyyar APC ta kammala shirya shaidu da kuma hujjojin bada kariya akan karar da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya shigar gaban kotu, inda yake kalubalantar yadda sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairun bana ya kasance.
A wani martani da jam’iyyar ta APC ta hannun Lauyanta Thomas Ojo ya gabatar,Ya baiyana cewar dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour,ba cikakken dan jam’iyyar ba ne har zuwa lokacin da aka yi zabe.
Bugu da kari jam’iyyar ta APC ta baiyana cewar tsohon gwaman na Anambra dan jam’iyyar PDP ne har zuwa ranar 24 ga watan Mayun 2022,kuma an tantance shi a matsayin daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar ta PDP, a cikin watan Afrilun 2022.
A saboda haka jam’iyyar ta APC ta ce Peter Obi bai cancanci ya kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa ba.