Jam'iyyar APC reshen jihar Kano tayi kira ga mambobinta da su tashi tsaye domin kare dimokradiyya da bangaren shari'a yayinda Jam'iyyar NNPP ta shirya zanga-zanga kan karar da har yanzu ba a yanke hukunci ba a kotun sauraron kararrakin zabe.
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar ta APC a jihar Kano Ahmad Aruwa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya.
Ya ce ‘ya’yan jam’iyyar APC suyi taka-tsan-tsan wajen tunkarar duk wata zanga-zangar adawa da dimokuradiyya da jam’iyyar NNPP za ta yi, yana mai jaddada cewa shirin zanga-zangar wani yunkuri ne da gangan na tsoratar da bangaren shari’a da kuma dakile tsarin dimokuradiyya da bin doka da oda da ‘yancin bangaren shari’a.
Aruwa ya ci gaba da cewa, jam’iyyar APC ta jihar Kano tana da yakini akan bangaren shari’a wajen gudanar da aikin bangaren, don haka ya tunatar da NNPP cewa duk abin da ya samu sakamakon hukuncin akwai kotun daukaka kara da kuma kotun koli.
Daga nan ya bukaci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC da su kasance cikin shiri tare da jiran karin umarni na gaba daga jam’iyyar.