A Kano, jam’iyyar APC ta nemi kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta ba su izinin duba kayan zaben da aka yi amfani da su a zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
A zaman da aka cigaba da gudanrwa, Lauyan masu shigar da kara, Nureini Jimoh SAN, ya bukaci kotun da ta baiwa wanda yake karewa damar duba kayan zaben da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben.
Sai dai Lauyan INEC, Mista K C Wisdom, ya shaida wa kotun cewa an basu sanarwa ne kawai a ranar Alhamis.
Lauyoyin Gwamna Kabir-Yusuf, Adegboyega Awomolo bai ki amincewa da bukatar ba.
Kwamitin mai mutane uku ya umarci duk masu shigar da kara da su kammala tattara bayanansu kafin a fara cikakken sauraron karar.
Kotun dai ta dage zaman har zuwa ranar 15 ga watan Yuni.