On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jami'ar Jihar Kaduna Ta Koma Bakin Aiki, Bayan Da Gwamnan Jihar El-Rufai Yayi Barazanar Korar Malaman dake Yajin Aikin ASUU

Gwamna El-Rufai Na Jihar Kaduna

Hukumar gudanarwar Jami’ar jihar Kaduna ta koma bakin aiki domin cigaba da zangon karatu na biyu na tsarin kalandar karatu ta shekarar 2020 zuwa 2021 ga dalibanta, bayan shafe sama da watanni biyar tana a kulle, biyo bayan yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’oi ta Kasa ASUU ta shiga.

Komawa bakin aikin, zai bada damar cigaba da rubuta jarabawar zangon karatu na biyu wadda aka dakatar da ita, a sakamakon tafiya yajin aiki da kungiyar ASUU tayi tun a cikin watan  Fabarairun  bana.

Mukaddashin Shugaban jami’ar jihar Kaduna, Farfesa Abdullahi Ashafa, Ya baiyana cewa  jami’ar  bata da wata matsala tsakaninta  da reshen kungiyar ASUU dake jami’ar, a saboda haka babu bukatar  kyale Dalibai su cigaba da zaman dirshan a gidajensu.

Kazalika yayi gargadin cewa akwai hukunci mai tsauri ga duk wani Dalibi ko kuma Malami da yaki komawa aji kamar yadda  hukumar gudanarwar jami’ar jihar Kaduna ta bayar da umarni.

Idan ba’a manta ba, Gwamna Nasir El-rufai’I Yayi barazanar Korar daukacin Malaman Jami’an jihar Kaduna, matukar suka ki komawa bakin aiki