Jami’ar Bayero dake nan Kano ta tsawaita wa’adin lokacin biyan kudin rijista ga Daliban makarantar da kimanin wata daya, Domin ganin dalibai ba su dena zuwa makaranta ba, a sakamakon karin kudin makaranta da aka yi.
Idan ba’a manta ba, Jami’ar ta Bayero ta sanar da karin kudin makaranta ga masu karatun Digiri da kuma babban digiri a jami’ar da kimanin sama da kaso 100 bisa 100.
Wata sanarwa da kakakin jami’ar Garba Lamara ya fitar a ranar Alhamis, Ta ce kara wa’adin biyan kudin makarantar ya biyo bayan rokon da gwamnatin jihar Kano da Kungiyoyin Dalibai da kuma Al’umma suka yi.
Ya ce a halin yanzu wa’adin biyan kudin makarantar zai kare daga tsakar daren 10 ga watan Satumbar bana. Kazalika ya ce jami’ar ta baiwa dalibai yan asalin jihar Kano guda 500 tallafin karatu sakamakon karin kudin makarantar da aka yi.