Jami’ar Bayero dake nan Kano, ta baiyana wasu rahotanni dake cewar an samu matsalar garkuwa da mutane ko kuma matsala ta rashin a jami’ar, a matsayin ‘karya da basu da tushe balle makama.
Wata sanarwa da mataimakin magatakardan jami’ar Bayero, Lamara Garba ya aikowa Arewa Radiyo a daren jiya, Ta jadadda cewar labaran na zuki ta malli ne.
Sanarwar ta baiyana cewar jami’ar ta yi matukar damuwa da yadda wasu mutane marassa zuciya zasu kirkiri labarin bogi, wanda suka san cewar zai haddasa rudani a cikin jami’ar ta Bayero dama jihar Kano baki daya.
Lamara Garba y ace jami’ar Bayero tana cikin aminci da kwanciyar hankali da zaman lafiya, a saboda haka jama’a suyi watsi da labarin da aka kirkira, wanda ke nuna an samu wata barazana ta rashin tsaro a jami’ar.