Jami’ar Bayero ta kare matsayar data dauka na kara kudin makaranta, Inda ta baiyana cewar karin ba shi da wata alaka da janye tallafin mai ko kuma baiwa dalibai lamunin Karatu.
Idan ba’a manta ba, A cikin mujallar dajami’ar ke wallafawa ta musamman,Mukaddashiyar Magatakardar jami’ar, Amina Umar Abdullahi, ta bada sanarwar yin karin kudin makarantar da kaso 100 bisa 100, ga masu karatun digiri da kuma babban digiri.
A yayin hirarsa da Arewa Radiyo, Kakakin jami’ar, Lamara Garba, Ya ce karin kudin makarantar na da alaka da umarnin da gwamnati mai ci ta baiwa manyana makarantu a kasar nan, kan cewar su nemi hanyoyin samun kudin shiga.
Sai dai ya ce duk da karin kudin makarantar wani babban nauyi ne ga dalibai, To sai dai kuma har yanzu, najeriya na cikin jerin kasashe masu saukin biyan kudin makaranta.
masu karatu a bangaren likitanci da sauran darussan kimiyya zasu rika biyan naira dubu 170 ga sabbin shiga sai kuma wadanda ke ciki zasu rika biyan naira dubu 160, yayin da sauran darussan zamantakewa, kamar fannin shari'a, da nazarin addinin musulunci za'a rika biyan naira dubu 97 ga daliban dake cikin jami'ar, saiu kuma sabbi zasu rika biyan naira dubu 105