Jami’ar Bayero dake Kano ta musanta rahotanni da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani da ke bayyana karin kudin makaranta.
Wata sanarwa da mataimakin magatakardar mai kula da harkokin yada labarai, Lamara Garba ya fitar ta ce wasikar da ake yadawa bata da tushe.
Sanarwar ta ce har yanzu mahukuntan jami’ar ba su yanke hukunci kan duk wani karin kudin makaranta ba sabanin yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta.
Ya bukaci dalibai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su lura cewa har yanzu Jami’ar Bayero ba ta yanke shawara kan karin kudin makaranta ba.