Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Taya Mamallakin Jami’ar Afe Babalola dake birnin Ado Ekiti tare da Hukumar gudanarwar Jami’ar da Daukacin Ma’aikatanta murnar matsayin da jami’ar ta samu, Na kasancewar ta a matsayin jami’ar data fi kowace Jami’a Daraja a kasar nan.
Wani rahoto na jami’oin duniya da aka fitar, Ya baiyana Makarantar a matsayin ta 400 a jerin Jami’oin da suka fi kwazo a fadin Duniya.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, Ya baiyana cewa, Shugaban kasar Yace, Tsari da kuma manufa tare da salon shugabanci da aka dora jami’ar a kai tun bayan shekaru 12 da kafuwar ta, sune abubuwan da suka kaita ga samun wannan matsayi.
Kazalika Shugaban kasar, Ya jinjinawar jami’ar game da irin tsare-tsare na samun ilimi mai inganci da kuma matakan ladabtarwa dana shugabanci da take dasu.