On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Jami'anmu Sun Maida Martani Ga 'Yan Ta'adda Da Suka Kai Hari Offishin INEC A Jihar Imo - Rundunar 'Yan Sanda

Rundunar 'yan sanda a jihar Imo ta ce jami’anta sun samu nasarar daƙile wani hari da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne tare da wata ƙungiya mai kawance da aka fi sani da ESN suka kai ofishin hukumar zabe ta kasa INEC na ƙaramar hukumar Orlu a jihar.

Rundunar ‘yan  sandan ta ce 'yan bindigar sun tsaya daga bayan katangar ofishin hukumar zaɓen tare da jefa abubuwan fashewa  cikin harabar ofishin acewar kakakin rundunar ‘yan sandan, Mike Abbatam.

Tunda farko kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe Festus Okoye  ya sanar da kai harin a daren ranar Juma’a.

Kakin ‘yan sandan, ya ce cikin ƙwarewar aiki jami'an 'yan sanda sun  martini kan harin, inda suka samu nasarar fatattakar 'yan bindigar bayan da da yawa daga cikinsu suka samu munanan raunuka.

Sanarwar ta ce 'yan sanda na gudanar da bincike domin ganowa tare da kama waɗanda ake zargi da kai harin offishin hukumar zabe a jihar ta Imo.