Jami’an hukumar tsaro dake bada kariya ga fararen hula Civil Defence reshen jihar Kano sunyi nasarar kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne.
Kamar yadda wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ibrahim Abdullahi ya fitar a ranar Laraba, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata a unguwar SabonGari da ke karamar hukumar Fagge.
Wadanda ake zargin sun hada da Faisal Usman mai shekaru 28 da Mansur Isa mai shekaru 38 da Abdullahi Bashir mai shekaru 25 da Ahmed Ibrahim mai shekaru 21 da Zulkifil Bello mai shekaru 25.
Sanarwar ta ce rundunar tana bin diddigin abokan aikinsu, Sunday da Abdullahi, wadanda suka saba sayarwa da wayoyi da layukan waya..