Gwamnatin kasar Amurka ta hannun hukumar dakile yafuwar cutuka ta kasar ta aiko da wata tawaga zuwa Najeriya domin sanin makamar aiki akan matakin kiwon lafiya da dakile cutuka da kuma matakan ko ta kwana.
Daraktan kula da harkokin lafiya a majalissar dinkin duniya Mr. Brian Massa, wanda ya jagoranci tawagar zuwa dakunan bincike da gwaje-gwaje kan cutuka a Abuja, yace jami’an suna ziyarar aiki a Najeriya ne domin sanin makamar aiki
Massa yace tawagar ta kewaya dakunan gwaje-gwajen tare da tattaunawa da tsarin kiwon lafiya da tattara bayanai da kuma yadda Najeriya ke tunkarar yaki da cutar Kyandar biri da ake fama da ita a yanzu haka.