On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Jami'an Tsaro Sun Hallaka Masu Garkuwa Da Mutane 60 A Jihar Bauchi - Gwamna Bala

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kashe mutane 60 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kubutar da mutane 29 a karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar.

Mohammed ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar Lere da ‘yan bindiga suka kai musu hari cikin ‘yan kwanakin nan.

Ya ce an samu nasarar hakan ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da ‘yan sa kai, da mafarauta.

Gwamnan ya ce rashin tsaro yana kara ta’azzara a jihar, kuma ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mohammed ya kuma bayar da gudummawar babura 30 da Naira miliyan 10 ga jami’an tsaro a yankin.