Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’oi da sauran manyan makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta bankado wata daliba mai suna Ejikeme Mmesoma da ake zargi da yin magudi tare da zama amatsayin wacce ta fi kowa cin maki a Jarrabawar shiga Jami’oi da manyan makarantu ta 2023 wato UTME.
Idan za’a iya tunawa Mmesoma, dalibar makarantar sakandaren ‘yan mata ta Anglican dake birnin Nnewi a jihar Anambra, ta bayyana cewa ta samu maki 362 a jarabawar UTME ta bana.
Hakan ya sa mai kamfanin Innoson Motors, Innocent Chukwuma, ya ba ta kyautar Naira milliyan 3 kuma gwamnatin jihar Anambra na shirin karrama ta.
Sai dai mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Fabian Benjaminin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa a zahiri dalibar ta samu maki 249 a jarrabawar tare da yin magudin sauran sakamakonta.
Hukumar ta sha alwashin janye sakamakonta tare da gurfanar da ita a gaban kuliya.