Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu Ta Kasa JAMB, Ta ja kunnen Masu cibiyoyin Na’ura Mai Kwakwalwa da ake rubuta jarabawar, Da su guji karbar kudi daga hannun masu rubuta jarabawar ko kuma su fuskanci Hukunci mai tsauri.
A mujallarta ta Mako-Mako da take wallafawa, Hukumar tace an jawo hankalinta game da yadda wasu masu wuraren cibiyoyin rubuta jarabawar, ke karbar sama da naira 700 daga hannun Masu rubuta jarabawar, da sunan biyan kudin aikin da suka yi masu.
Hukumar tace ba zata saurarawa duk wanda aka samu da aikata lefin karbar kudi ba, sannan kuma zata ci tarar naira dubu 100 aka duk wanda aka samu da aikata wannan lefi.
Daga nan Hukumar JAMB ta shawarci masu rubuta jarabawar ta da su kai rahoton duk wata cibiyar na’ura mai Kwakwalwa da aka samu tana karbar kudi fiye da naira 700 da sunan kudin aiki.