Hukumar shirya jarabawar shiga Jami'ai da sauran makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ta kara kudin rajistar shekarar 2024.
Mai baiwa hukumar shawara kan harkokin yada labarai, Dr Fabian Benjamin, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Laraba.
A cewar Benjamin, bayanan sun sha bamban da gaskiya saboda kudin da ake kashewa wajen Rijistar UTME na hukumar har yanzu dubu 3 da 500 ne.
Benjamin ya kara da cewa sabanin jita-jitar daya daga cikin matakan da Hukumar ta yi la’akari da su shi ne rage farashi a duk wani abu da ya shafi jarabawar ba ya ga kudin rijista.