Mutanan yankin chiranchi makaranta sun koka sakamakon gina shaguna a jikin makaranta sekandere mata ta chiranchi wanda matasan yankin suka fito domin nuna rashin goyan bayansu ga gina shagunan.
Kazalika mutanen sun baiyana bukatar a gyara makarantar a maimakon gina shaguna wanda ba sune makarantar ke bukata a halin yanzu, in banda abubuwan zama da karin a jujuwan karatun dalibai da sauran gyare-gyare makaranta wanda dalibai sama da dari ke karatu cikin aji daya.
Mutanen yankin sunyi kira ga gwamnatin idan har sai anyi shagunan to a mallakawa makarantar su domin bunkasa mata hanyoyin samun kudin shiga.
Wakilinmu Ado Danladi Farin Gida ya tuntub Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta jihar Kano wanda suka ce Ma’aikatar ilimi ce ke da alhalin yin magana akan al’amarin, sai dai koda aka tuntubi ma’aikatar Ilimin itama tace hurumin hukumar kula da makarantun Sakandire ce.