On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jahohin Najeriya 19 Da Garuruwa 56 Na Cikin Hatsarin Ambaliyar Ruwa A Damunar Bana - NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta yi gargadi, cewa jihohi 19 da garuruwa 56 a sassa daban-daban na kasarnan, za su fuskanci mamakon ruwan sama, wanda zai iya haddasa ambaliya a cikin wannan wata na Agusta.

A wata zanatawa da BBC, babban jami'in kai dauki na hukumar NEMA, Bashir Idris Garga, ya bukaci jama'a, musamman ma wadanda ke zaune a wuraren da abin zai shafa da su zauna cikin shiri.

Ya ce  gardagin ya biyo bayan hasashen da hukumar yanayi ta kasa ta fitar.

Yace tun daga 14 zuwa 18 kamar yada hasashen yanayin na watan Agusta na wannan shekarar ya nuna, za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Hukumar ta NEMA ta ce jihohin da al’amarin zai shafa sun hada da Delta da Ekiti da Ondo da Lagos da Anambra da kuma Ogun.

Sauran su ne Nasarawaa, Cross River  da Bauchi da Jigawa da Osun da Zamfara da Sokoto da Adamawa da Taraba da Binuwai da Imo da kuma Abia.

Hukumar tace ruwan sama  zai shafi garuruwa 56 dake cikin wadannan jihohi kuma tuni ta bukaci  gwamnattoci da su dauki matakai na musaman.