Dakarun sojin da suka yi Juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sunyi barazanar kashe Hambararren Shugaban Kasar Mohammed Bazoum, idan har wasu Sojojin suka afka masu da yaki.
Jagororin Juyin mulkin sunyi barazanar halaka hambararren Shugaban, Muddin kasashen da take makwabtaka dasu suka yi yunkurin afka mata da yaki, domin mayar da shugaban kasar kan kujerarsa.
Jaridar Daily mail ta ambato wasu jami'an Kasar na baiyana haka ga wani babban jami'in diflomasiyyar kasar Amurika.
A jiya ne kungiyar Raya tattalin arzikin yammacin kasashen Afrika, ECOWAS ta umarci kwamitin ta na tsaro da ya shiryawa dakarunsa damarar yaki domin kasancewa cikin shirin ko ta kwana. Inda kungiyar ta yi All..h wadai da cigaba da tsare Bazoum tare da iyalansa.
Rahotanni sun baiyana cewar Sojojin da suka yi Juyin mulkin sunyi barazanar kashe Mohammed Bazoum, kamar yadda suka fadawa mataimakiyar Sakataren harkokin wajen Amurika Victoria Nuland, yayin ziyarar da ta kai Kasar a karshen mako.
Kanfanin dillancin Labarai na AP ya tabbatar da faruwar hakan.